ECOWAS ta yanke shawarar rage dakarun soji a Gambia

Gambia

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ranar Alhamis Mista Barrow ya isa Gambia daga kasar Senegal

Kasashen Afrika ta Yamma na shirin rage yawan dakarun sojin da suka tura Gambia domin tabbatar da cewa Shugaba Adama Barrow ya hau ragamar mulki bayan da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya ki yarda da shan kaye a zaben ranar 1 ga watan Disamba.

Kwamnadan rundunar, Janar Francois Ndiaye, ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP hakan.

A wata sanarwa, Janar Ndiaye ya ce yanayi ya inganta, lamarin da ya sa aka yanke shawarar rage yawan dakarun.

AFP ya kuma ambato sanarwar tana cewa za a dan rage yawan dakarun ruwa da na sama.

Janar Ndiaye ya ki bayyana yawan sojojin da ke cikin kasar ta Gambia, amma a baya shugaban hukumar kungiyar ECOWAS, Marcel Alain de Souza, ya bayyana cewa dakaru 4,000 aka tura daga cikin 7,000 da aka shirya turawa daga kasashe biyar, ciki har da Senegal, da Najeriya, da Ghana.

Ranar Asabar Mista Jammeh ya bar kasar bayan matsin lamba ta fuskar diflomasiyya da barazanar da ECOWAS ta yi ta kama shi.