Shugaba Trump da Theresa May za su hada kai don yaki da kungiyar IS

Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Theresa May da Donail Trump a taron manema labarai

Firai ministan Burtaniya, Theresa May, ta zama Shugabar wata kasa ta farko da ta fara ganawa da Shugaba Donald Trump tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Amurka.

Kuma bayan tattaunawarsu a fadar White House a ranar Juma'a, Mista Trump ya yaba da dangantaka ta musamman da ke tsakanin Amurka da Birtaniya.

Misis May ta ce za su yi aiki tare da shugaba Trump domin kawar da kungiyar IS, inda suka sake jaddada goyon bayansu ga kungiyar tsaro ta NATO.

Haka kuma Firai ministar ta yi alkawarin kara wa kasashen Turai kwarin guiwar kara kashe kudi kan harkar tsaro.