'Shugaba Assad lafiya kalau yake'

Shugaban Syria Bashar al-Assad

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Gwamnatin Syria ta ce Bashar al-Assad lafiyarsa kalau, ba wata larurar kwakwalwa ko shanyewar jiki da ya gamu da ita

Gwamnatin kasar Syria ta yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa Shugaba Bashar al-Assad ba shi da lafiya, ta ce lafiyarsa sumul ba wata larura da yke fama da ita.

Hukumomin kasar sun ce Shugaba Assad yana nan cikin koshin lafiya, ya na kuma gudanar da harkokinsa na yau da kullum.

A wata sanarwa da fadar gwamnatin ta fitar, ta ce jita-jitar zuki-ta-malle ce kawai, da wasu suka shirya dan karfafa wa makiyansa gwiwa.

Wasu rahotanni daga kafafen yada labarai na kasashen Larabawa na nuna cewa kwakwalwarsa ta tabu bayan shekara shida ana yakin basasa.

Wasu kuma na bayyana cewa ya gamu da larurar shanyewar jiki, abin da hukumomin kasar suka ce duka karerayi ne kawai.