Wasu amsoshin tambayoyinku kan akidun Trump

Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tuni Mista Trump ya fara sanya hannu kan wasu dokoki

Mutane a Amurka da ma duniya baki daya za su so jin amsar tambayoyi kan wasu batutuwa kamar makomar 'yan gudun hijira da Musulmai a Amurka da auren jinsi da dumamar yanayi da katangar Mexico da sauransu.

Ga dai amsar wasu tambayoyin da watakila kun sha tambayarmu a shafukan sada zumunta da muhawara ko kuma kuna tambayar kawunanku

Ko Trump zai fatattaki 'yan gudun hijira?

Bayan kwana biyar da darewarsa shugabancin Amurka, Mista Trump ya shaida wa wani manemin labari na CBS cewa zai mayar da ko ya daure 'yan gudun hijira miliyan biyu ko miliyan uku.

Wadanda yake fako sun hada da 'yan ci ranin da aka taba kamawa da aikata miyagun laifuka da jagororin munanan kungiyoyi da kuma masu fasa-kwaurin miyagun kwayoyi.

Akwai kusan 'yan ci-rani miliyan 11 da suke zaune a Amurka ba bisa ka'ida ba, kuma Mista Trump ya wallafa wani tsari mai manufofi 10 a kan ci-rani da suka hada da sauya wasu tsare-tsaren tsohon shugaban kasar Barack Obama a kan 'yan ci-rani da tsaurara matakan shige da fice da kuma mayar da wadanda basu da cikakkun takardun zama kasashensu.

Tun a ranar farko ta shigarsa ofis, Mista Trump ya fara amsa wannan tambaya, inda ya ce zai sanya hannu a kan kawar da ''yan ci-ranin da suke zaune a kasar ba bisa ka'ida ba', zai kuma daure duk mutanen da ya kama suna shiga Amurka ba bisa ka'ida ba sannan daga bisani ya mayar da su inda suka fito.

Ya kuma yi alkawarin kara yawan jami'an kula da shige da fice don ya cimma wannan fata nasa.

Tuni dai har Mista Trump ya bayyana cewa ba zai karbi bakuncin Musulmai 'yan gudun hijirar Syria ba, amma zai karbi na takwarorinsu Kiristoci.

Ya kuma umarci a fara hana kudade isa ga wasu biranen Amurka da ke faran-faran da bakin haure.

Yaya Musulmai za su samu kansu?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Akwai miliyoyin Musulmai a Amurka

Shin idan kai Musulmi ne za ka iya cigaba da zuwa Amurka shakatawa?

Tun bayan harbe-harben da aka yi a jihar California a 2015 inda mutane 14 suka mutu, Mista Trump ya yi kira da a hana Musulmai shiga Amurka kwata-kwata, 'har sai wakilan kasar sun gano me yake faruwa.'

Batun nasa ya jawo ce-ce-ku-ce a duniya har da ma mataimakinsa Mike Pence, wanda ya ce 'kalamin bai dace ba kuma ya kaucewa kundin tsarin mulkin kasar.'

Bayan 'yan watanni sai Mista Trump ya sauya kalamansa nasa, har ma aka cire kalaman daga shafinsa na intanet.

Sai dai ga shi tun tafiya ba ta yi nisa ba, cikin mako na biyu da darewarsa mulkin, Mista Trump ya dakatar da wasu kasahsen Musulmai bakwai daga shiga Amurka kwata-kwata. Kasashen sun hada da Iraki da Iran da Yemen da Syria da Somaliya da Sudan da kuma Libiya.

Ga alama dai da sauran rina a kaba don wannan al'amari na iya shafar wasu kasashen Musulman ma nan gaba, wata kila har da 'yan Afirka ko 'yan kasa irin Najeriya.

Kuma kamar yadda aka sani Najeriya na daga cikin kasashen da take da rinjayen Musulmai.

Me ye tunaninsa game da Afirka?

Amurka na kashe biliyoyin daloli don zuba jari da ayyukan jin kai a Afirka, amma Donald Trump bai bayyana wasu kwararan manufofi kan yadda zai yi mu'amala da nahiyar ba.

Sai dai bai boye aniyarsa ta son ganin duk wani dari da kobo an kashe shi a inganta Amurka ba maimakon kai wa wasu kasashen.

Su ma masu fafutukar ganin sun balle daga Najeriya don samun jamhuriyar Biafra, sun nuna goyon bayansu ga Mista Trump, da tunanin watakila zai marawa fafutukarsu baya.

Sai dai har kawo yanzu bai ko nuna alamun yin wata magana mai kwari da ta danganci Najeriya ko ma Afirka gaba daya ba.

Yaya za a kare da batun auren jinsi?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Trump ba ya goyon bayan auren jinsi

Shin za a ci gaba da batun auren jinsi wanda Mista Obama ya halatta ko kuwa?

Duk da cewa Mista Trump ya ce ya taba halartar wani auren jinsi, amma karara ya nuna adawarsa da wannan manufa cikin hirarrki da dama da aka yi da shi.

Batun auren jinsi baya daga gaba-gaba cikin muradunsa, amma akwai kwararun alamun cewa zai iya soke shi.

Ko zai ci gaba da harkokin kasuwancinsa?

A wata hira da tashar CNN ta yi da lauyansa ya ce Mista Trump zai danka al'amuran kula da kasuwancinsa ne a hannun manyan 'ya'yansa Donald Junior da Ivanka da kuma Eric.

Kasuwancin Mista Trump sun hada da otal-otal da wuraren wasan kwallon golf da gidajen haya da manyan kamfanoni da sauransu.

Tuni ma dai har an ga yadda a yanzu ya mayar da hankalinsa kacokam kan ragamar mulkin fiye da kasuwancin nasa.

Yaushe za a fara gina katanga tsakanin Amurka da Mexico?

A lokacin yakin neman zaben Amurka dai, Mr Trump ya soki 'yan ci ranin Mexico inda har ya yi alkawarin cewa zai gina katanga a tsakanin kasashen, kuma Mexicon ce za ta biya kudin.

Bayanan hoto,

Tsawon katangar zai kai mil dubu biyu.

Sai dai kuma wani wakilin BBC ya ce duk da wadannan kalamai na Mr Trump, Mexico ta kasance babbar abokiyar huldar Amurka, inda suke kasuwancin biliyoyin daloli a duk shekara a tsakaninsu.

A iya cewa Mista Trump bai yi kasa a gwiwa ba, don kuwa tuni har ya sanya hannu kan kudurin da zai bayar da dama a fara gina kantangar a kan iyakar kasar da kudancin Mexico.

Ko zai haramta zubar da ciki?

A watan Maris din 2016 ne Mista Trump ya ce zai haramta zubar da ciki kuma zai sanya hukunci ga masu yi.

A wan Nuwamba kuwa aka samu karuwar bayar da taimako ga daya daga cikin manyan kungiyoyin da ke taimakawa wurin zubar da ciki, Planned Parenthood, sakamakon zaben Donald Trump da mataimakinsa a matsayin shagube a gare su.

A ranarsa ta farko da shiga ofis, Mista Trump ya sanya hannu a kan dokar da ke jaddada hana Amurka ta bai wa kungiyoyin kasashen duniya da ke goyon bayan ko tattaunawa kan zubar da ciki a matsayin wani zabi na tsarin iyali.

Wannan alama ce da ke nuna bai sauya ra'ayi kan haramta hakan ba.

Mene ne matsayarsa a kan yarjejeniyar sauyin yanayi?

Tuni ya nuna kin goyon bayansa kan batun sauyin yanayi ya kuma nuna son janye Amurka daga yarjejinyar sauyin yanayi ta Paris.

Ya ce yarjejeniyar ba za ta haifarwa Amurka alheri ba kan harkokin kasuwancinta sai dai ma ta bai wa gwamnatocin kasashen waje damar kayyade adadin makamshin da 'za mu yi amfani da shi.'

Bayanan hoto,

Ba ya son goyon bayan sauyin yanayi

Shin Trump zai rage wa kungiyar Nato karfi?

Duk da cewa bai tabo wannan batu ba tun bayan shan rantsuwar mulki, ga alama nan gaba kadan zai waiwayi batun

Karara ya nuna cewa Amurka ce gaba da komai a wajensa, don haka dole ya kare muradunta. Ya ce sauran kasashe kawayen Amurka su ya kamata su dinga daukar nauyin kudaden ayyukan soji a kungiyar tsaro ta Nato.

Yanzu dai a iya cewa cikakkun amsar wasu tambayoyin za a jira har zuwa nan da wani dan lokaci kafin a gama gane inda Mista Trump ya sa gaba sosai.

Sai dai zuwa yanzu yana ta shan suka kan wasu matakan da ya riga ya fara sanyawa hannu.