Serena Williams ta doke 'yar uwarta Venus

Serena

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Serena ta kafa tarihi

Serena Williams ta doke 'yar uwarta Venus ta lashe gasar tennis ta Australian Open karo na bakwai a jere sannan ta kafa tarihin cinye Grand Slam na 23 a rukunin 'yan ɗai-ɗai.

Serena, mai shekara 35, ta yi nasara da ci 6-4 6-4 inda ta zarta Steffi Graf wajen kafa tarihi tun da aka amince da kwararrun 'yan wasan Grand Slams a shekarar 1968.

'Yar kasar ta Amurka ta karbe mataki na farko ne daga hannun 'yar kasar Jamus Angelique Kerber.

'Yar kasar Australia Margaret Court, ita ce kadai 'yar wasan tennis da ta zarta Serena a Grand Slam na 'yan daidai.

Venus ta taya Serena murna a kan nasarar da ta yi, tana mai cewa "ina taya ki murna, Serena, bisa yin bajinta ta 23."