Trump ya sa an tsare wasu Musulmi a filin jirgin saman Amurka

An saki Haneed Khalid Darweesh

Asalin hoton, @NydiaVelazquez

Bayanan hoto,

An saki Haneed Khalid Darweesh

Ana ci gaba da tsare 'yan gudun hijirar da ke shiga Amurka a filin jiragen saman kasar bayan Shugaba Donald Trump ya bayar da izinin hana Musulmi shiga kasar.

Masu zanga-zanga sun taru a filin jirgin saman John F Kennedy da ke birnin New York inda suka bukaci a saki 'yan gudun hijira 11 wadanda ake tsare da su a can.

Har yanzu dai ba a san irin tasirin da umarnin da Shugaba Trump zai yi ba.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama sun gurfanar da shi a gaban kotu a kan batun.

An haramtawa mutanen da ke tserwa daga rikicin Syria shiga Amurka har sai yadda hali ya yi.

Sauran 'yan kasashen da aka hana shiga Amurka su ne Iran, Iraq, Libya, Somalia, Sudan da kuma Yemen.

A yayin da aka tsare mutanen da ke shiga Amurka 'yan kasashen da aka ambata, ana sauke wadanda ke shiga jirgi domin zuwa Amurka daga kasashen ko da kuwa suna da cikakken izinin zama a kasar.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam, cikin su har da the National Immigration Law Centre (NILC) da the American Civil Liberties Union (ACLU), sun kai karar Trump a wata kotun New York domin bukatar a saki wasu 'yan kasar iraqi guda biyu wadanda ke shirin sake shiga Amurka.

Daya daga cikin su, Haneed Khalid Darweesh, wanda yake aiki a matsayin tafinta a rundunar sojin kasar ya samu 'yanci ranar Asabar inda aka sallame shi.

Sai dai ana ci gaba da tsare daya mutumin, Haider Sameer Abdulkhaleq Alshawi.

Asalin hoton, Getty Images