Wata kotu ta dakatar da Trump daga korar Musulmi

Big crowds at JFK

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Filin jirgin saman JFK da ke New York na cikin wuraren da masu zanga-zangar suka yi wa tsinke

Wata mai shari'a a babbar kotun Amurka ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da matakin nan na Shugaba Donald trump na korar 'yan kasashen wajen da ke dauke da takardun izinin zama a Amurka.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta The American Civil Liberties Union (ACLU) ce ta kai shi karar domin a hana shi aiwatar da matakin da ya dauka.

Kungiyar ta ce matakin da kotun ta dauka ya haramtawa gwamnati Amurka fitar da mutanen daga kasar.

Kungiyar ta yi kiyacin cewa an tsare akalla mutum 100 zuwa 200 a filayen jirgin saman Amurka.

Matakin da kotun ta dauka ya zo ne a daidai lokacin da daruruwan masu zanga-zanga suka mamaye filiyen jirgin saman kasar domin nuna bijirewarsu kan hana wasu 'yan gudun hijirar da ke dauke da takardar izinin shiga kasar.

Mai shari'a Ann Donnelly ta hana fitar da dukkan mutanen da ke da bisar zama a kasar da "sauran mutanen da ke da izinin shiga Amurka".

Lee Gelernt, mataimakin daraktan wani shiri na kare hakkin 'yan gudun hijira, ya ce matakin da kotun ta dauka ya sa mutane sun yi ta sowa da murna.

Ya kara da cewa an yi wa wasu 'yan gudun hijirar barazanar saka su a jirgi domin fitar da su daga kasar.

Yanzu dai kotu ta tsayar da watan gobe domin ci gaba da sauraren karar.