Malaysia: 'Yan yawon bude ido 31 sun bata

Malaysia Coast

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gabar tekun Malaysia na jan hankalin 'yan yawon bude ido

Hukumomin kula da teku na Malaysia sun ce wani kwale-kwale mai dauke da mutum 31 ya bata a gabar tekun kasar.

Ba a sake jin duriyar kwale-kwalen ba tun bayan da ya bar jihar Sabah a ranar Asabar.

Hukumar kula da harkokin sufurin teku ta Malaysia ta ce mummunan yanayi na jawo tsaiko wajen neman jirgin.

Mutum 28 daga cikin 31 da ke cikin kwale-kwalen 'yan kasar China ne masu yawon bude ido.

Lamarin ya zo daidai da ranar farko ta sabuwar shekarar China, wadda 'yan kasar - mazauna Malaysia ke bikin murnar zagowarta.

Kwale-kwalen ya bar garin Kota Kinabalu ne a ranar Asabar da safe don zuwa Pulau Mengalum, wani sanannen waje da masu yawon bude ido kan ziyarta.

Hukumar kula da harkokin sufurin tekun Malaysia din ta ce ta samu kiran waya daga jirgin amma kuma daga bisani sai layin ya yi wahalar samu.

Ministan yawon bude ido na jihar Sabah, Masidi Manun, ya ce, ''Ina son shaida wa 'yan uwan wadanda suke cikin jirgin cewa ana ci gaba da kokarin neman su don a ceto su.''

Ruwan sama mai tsanani da ake yawan samu a daidai wannan lokaci na shekara ne yake kawo matsala wajen kokarin neman kwale-kwalen.