Mayakan BH sun kashe wasu daliban jami'ar Maiduguri

Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a kwanakin nan duk da kokarin da sojin Najeriya ke yi don fatattakarsu

Rahotanni daga jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya na cewa wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun far wa wasu matafiya a kan hanyar Maiduguri zuwa jihar Taraba, inda suka kashe mutane da dama ciki har da wasu daliban jami'ar garin.

Mayakan sun budewa motar wuta ne wanda ya tilastawa direban motar tsayawa, wasu fasinjojin suka ranta a na kare wasu kuma al'amarin ya ritsa da su.

Daga cikin mutanen da suka mutu din akwai daliban jami'ar Maiduguri, wadanda suke kan hanyarsu ta komawa garuruwansu sakamakon kammala jarrabawa da rufe makaranta da aka yi.

Wani Malamin jami'ar ya shaidawa BBC cewa zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar dalibai biyu daga ciki, yayin da wasu uku kuma suna babban asibitin koyarwa na Maiduguri.

"Ba mu dade da dawowa daga jana'izar daya dalibin ba, dayan kuma yanzu wasu Malaman da kuma babban jami'i na jami'a mai kula da harkokin dalibai suka tafi asibiti don karbo tasa gawar," inji Malamin.

Baya ga daliban jami'ar akwai kuma wasu mutane da suka mutu wadanda ba a san adadinsu ba zuwa yanzu.

Ko makwanni biyu da suka gabata ma kungiyar Boko Haram ta kai wasu hare-hare jami'ar Maidugurin, wanda har ya yi sanadiyar mutuwar wani Farfesa da kuma wasu mutum hudu.

A sakamakon haka har hukumar jami'ar ta bayar da sanarwar ɗage jarrabawar ɗalibai da aka tsara za a fara a cikin makon.

Wancan hari shi ne karo na farko da ƙungiyar Boko Haram da kai hari kai tsaye a jami'ar ta Maiduguri.

Daga bisani kungiyar ta Boko Haram ta fitar da sanarwar cewa ita ce ta kai harin.