An harbe wasu mutane a masallacin Canada

'Yan sanda ba su bayar da cikakken bayani kan harin ba

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan sanda ba su bayar da cikakken bayani kan harin ba

Rahotanni daga Canada na cewa an harbe har lahira akalla mutum biyar a wani masallaci da ke birnin Quebec.

'Yan sanda sun ce an yi ta harbe a cikin masallacin ne ranar Lahadi da daddare.

Cibiyar ta wallafa hoton 'yan sanda a shafinta na Facebook a wajen masallacin, inda ta ce "wasu mutane sun mutu".

'Yan sanda sun ce an kama mutum biyu, amma ba su fadi adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata ba.

Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa 'yan bindga uku ne suka kai harin. Kamfanin ya ce mutanen da suka kai harin na dauke da manyan makamai, kuma an gan su lokacin da suke shiga masallacin.

Wata jaridar da ake wallafawa a yanki Le Soleil ta ce ta samu wasu rahotanni da ke cewa daya daga cikin maharan dan shekarar 27 kuma an kwace bindiga samfurin AK-47 daga hannunsa.

Amma 'yan sanda ba su yi cikakken bayani ba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan sanda sun kama mutum biyu