Za mu dauki 'yan gudun hijira aiki — Starbucks

Howard Mista Schultz

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Howard Schultz ya ce za i taimaki 'yan gudun hijira Musulmai da matsuguni

Kamfanin sayar da gahawa da shayi na Starbucks ya yi alkawarin daukar 'yan gudun hijira 10,000 daga sassan duniya daban-daban aiki a cikin shekaru biyar masu zuwa.

Kamfanin ya dauki wannan mataki ne a wani martani a kan aniyar shugaban Amurka Donald Trump ta korar 'yan gudun hijira da Musulmai daga kasarsa.

Howard Mista Schultz, shi ne shugaban kamfanin kuma ya rubutawa ma'aikatansa wata wasika wadda a cikinta yake cewa matakin da shugaba Trump ya dauka ya jawo "rikici da mamaki da kuma suka".

Ya kara da cewa kamfinin zai fara daukar ma'aikata a Amurka kuma zai mayar da hankali ne kan mutanen da suka yi aiki da soja ko kuma suka basu goyon baya.

Mista Schultz ne shugaban kamfani mai zaman kansa da ya soki anniyar Trump din a baya-bayan nan.

Manya kamfanonin Silicon Valley da ke Amurka wadanda suka hada da kamfanonin Facebook da Google da Tesla sun yi ta aike jawabai a kan batun, yayin da shi kuma kamfanin jiragen sama na Airbnb ya dauki nauyin bayar da matsuguni ga mutanen da takunkumin ya shafa da kuma wadanda suka kasa shiga Amurka.

A ranar Juma'a ne dai Mr Trump ya sanya hannu a kan wasu shirye-shiryensa da suka hana bai wa 'yan gudun hijira izinin shiga kasar nan da kwana 120, sannan aka haramta wa 'yan gudun hijirar Syria shiga Amurka kwata-kwata, kana aka dakatar da 'yan kasashe bakwai na Musulmai daga shiga kasar tsawon kwana 90.

Shugaban kamfanin Starbucks ya ce ya yanke wannan hukunci ne domin tarba da kuma taimakon mutanen da suke tserewa daga kasashensu saboda yaki da rikici da kuma karrama su don wariyar da ake nuna musu.

Kamfanin Starbucks dai yana da rassa sama da dubu 25,000 a kasashen duniya 75.