Philipines ta yi watsi da yaki da miyagun kwayoyi

shugaba Rodrigo Duterte

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An kashe sama da mutum 7,000 tunda da kasar ta fara yaki da miyagun kwayoyi

'Yan sandan kasar Philipines sun dakatar da yaki da miyagun kwayoyi mai cike da ce-ce-ku-ce a kasar har sai an magance matsalar karbar hanci da rashawa da ta dabaibaiye hukumar yan sandan kasar.

A ranar Litinin ne shugaban 'yan sandan Ronald dela Rosa ya ce za a wargaza sashen da ke yaki da miyagun kwayoyi na hukumar.

Wannan mataki dai ya zo ne a dai-dai lokacin da aka kashe wani dan kasuwa dan kasar Korea ta Kudu a hedikwatar 'yan sandan.

'Yan sandan da ke aiki a sashen yaki da miyagun kwayoyi ne suka sace kuma suka kashe shi.

An kashe sama da mutum 7,000 tun bayan da kasar ta dauki aniyar yaki da miyagun kwayoyi.

Mace-macen da aka samu da kuma tsauraran matakai da shugaba Rodrigo Duterte ya dauka ya jawo suka sosai daga kungiyoyin kare hakkin bil'adama da kasashen Yamma, duk da dai shugaban na ci gaba da samun goyon bayan 'yan kasar.

A lokacin da ya ke wani jawabi a ranar Litinin Mista Dela Rosa, ya ce, ''Mista Duterte ya umarce mu da mu fara tsaftace hukumar".

Ya ce, "Za mu tsaftace matsayin jami'an da muke da su a hukumar, watakila bayan haka, za mu iya komawa yaki da miyagun kwayoyi".

Da farko dai ya yi alkawarin kawar da matsalar zuwa watan Disambar 2016, amma kuma sai ya dage wa'adin zuwa Maris din shekarar 2017.

A yammacin ranar Lahadi ne ya shaida wa manema labarai cewa, "Zan dage wa'adin har zuwa rana ta karshe na mulkina, ba zan yi amfani da wa'adin watan Maris da na ambata a baya ba.''

Yaki da kwayoyi na daya daga cikin batutuwan da shugaban kasar Philippines ya fi mayar da hankalin a kai.