Magungunan cancer sun kara tsada a duniya

maganin cancer na tamoxifen

Asalin hoton, Science Photo Library

Bayanan hoto,

Ana amfani da maganin tamoxifen wajen magance sankarar mama

Wani bincike da kungiyar da ke yaki da cutar cancer ta turai ta yi ya nuna cewar farashin magungunan cance ya yi tashin gwauron zabi a cikin shekaru biyar da suka wuce.

Binciken ya nuna cewa tashin farashin yasa asibitoci sun taikata bai wa masu amfani da tsarin inshorar lafiya magungunan.

Farashin magungunan cancer irinsu tamoxifen da bulsufan sun ninka kudinsu sau goma.

Ma'aikatar lafiya ta Birtaniya ta ce zata yi iya kokarinta domin rage farshin magungunan.

Masu binciken sun ce yarjejeniyar da hukumar da ke kula da tsarin inshorar lafiya ya yi da kamfanonin magunguna bai hada da farashi ba, kuma samun magunguna a farashi mai rahusa zai taimaka wa masu fama da cutar da dama da ma magunguna na zamani.

Sun yi kiyasin cewa a duk shekara, hukumar kula da tsarin inshorar lafiya na kasar na kashe fam miliyan £380 a kan magungunan cancer.

Dalilin tsadar magungunan

Magungunan suna yin tsada ne idan ya kasance kamfani daya ne kawai yake samar da maganin kuma shi kadai aka yadda ya bayar a asibitoci.

Kamfanonin suna samun riba a lokutan da suka yi bincike a kan magungunan da ayyukan da za su inganta ci gaba a wurin samunsu.

Idan wa'adin da aka bai wa kamfanin ya kawo karshe kuma aka fara sayar da na wasu kamfanonin, kamata ya yi farashin ya ragu.

Duk da haka, saboda tsadar farashin magunguna, ba safai tsarin inshorar lafiya ke amincewa da amfani da sabbin magungunan cancer ba.

Takaitakata kulawa ga sabbin kamu

Dakta Andrew Hill, babban likitan magunguna ne da ke jami'ar Liverpool a Ingila da Melissa Barber da ke makarantar koyon tsafta da magunguna sun tattaro farashin magunguna da ke tsarin inshorar lafiya da za su gabatar a wurin wani taro da za a yi a kan cancer.

Sun gano cewa, kwayar farashin maganin Busulfan daya, wanda ake magance cancer ta jini da shi ya kai kusan fam daya a shekarar 2011 da kuma sama da fam biyu a shekarar 2016.

Tamoxifen, shi ne maganin da masu sankarar mama ke amfanin da shi, shima farashin kwaya daya ya kusa fam daya a shekarar 2011 da kuma sama da fam daya a shekarar 2016.

Asalin hoton, Getty Images

Abin damuwa

Dakta Hill ya ce ya matukar yin mamaki da ya gano cewar kamfanoni suna yawan kara farashin magungunan cancer.

"Mun gano cewa wasu kamfanoni su kan karbe ikon magungunan cancer na gama gari sannan, sannu a hankali su rika kara farashin," a cewar Dakta Hill.

Ya ce wannan abin damuwa ne, mussaman idan asusun kudin magungunan cancer na cikin matsin lamba sakamakon hauhawar farashin.

Amma Warwick Smith, darakta-janar na kungiyar samar da magungunan cancer na gama gari ya ce kudaden da asibitoci ke biya ba su kai yawan farashin na kamfini ba.

Ya kara da cewa kudin Tamoxifen miligram 10 da asibitoci ke biya sama da fam hudu ne ga ko wane fakiti mai dauke da kwayoyi 30 ko kuma kasa da fam daya ga ko wanne kwaya daya.

Muhimmin tanadi

Gasa a kasuwar magungunan cancer na gama gari ya haifar da muhimmin tanadi ga hukumar tsarin inshorar lafiya, kuma ya bai wa masu fama da cutar damar samun magunguna kamar Tamoxiffen wanda ake amfani da shi wajen rage hadarin kamuwa da sankarar mama ba wai kawai magance shi ba.

A magungunan gama gari wadanda ake amfani da su a asibitoci, yana da matukar amfani a babanta tsakanin farashin kamfani da kuma wanda ake saka wa daga baya.

Birtaniya ta gabatar da wani sabon kudirin doka ga majalisar kasar domin sa ido kan farashin da masu bayar da magunguna da kayan amfanin asibitoci ke yi nan gaba.

Sakamakon kudirin dokar, kamfanonin da aka kama da tsawwala farashin ba tare da wata kwakwarar hujja ba, za a kai karar su wajen hukumar da ke kula da gasa a tsakanin kasuwanni, kuma akwai yiwuwar za a ci tararsu.

Wasu kasashen turai ma sun dauki matakai makamanta haka.

A kasar Spaniya da Italiya, kin amincewa da farashin magungunan cancer na gama gari daga wajen kamfanonin ya jawo gargadi daga wajensu inda suke cewa za su iya dakatar da raba magungunan.

Dr Hill ya ce, "Wannan lamari abin damuwa ne duba da cewa ana cikin wani lokaci ne da masu fama da cutar ke samun tsawon rayuwa da kyakkyawar rayuwa sakamakon ingantanccen magani.