OIC ta yi tir da matakin Trump

mambobin kungiyar OIC

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sakatare janar na kungiyar OIC ya ce matakin zai kara dagula kalubalen 'yan gudun hijira

Kungiyar hadin kan kasashen Musulmai OIC, ta nuna damuwarta a kan matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na hana wasu kasashe bakwai mambobinta shiga kasar.

Sakatare janar na kungiyar OIC ya ce matakin zai kara dagula kalubalen 'yan gudun hijira da ake fama da shi. Wannan matakin ya shafi mutane da dama wadanda ke tserewa daga kasashensu saboda tsananin yaki.

"Irin wannan wariya da ake nunawa tsakanin al'ummomi zai kara rura wutar rikici da ta'adanci ne kawai a wani muhimmin lokaci da kungiyar OIC ta hada kai abokan hulda wanda ya hada da Amurka, domin shawo kan masu tsaurin ra'ayi da 'yan ta'ada ta kowane bangare," Inji shi.

OIC ta yi kira ga gwamantin Amurka da ta duba yiwuwar sauya shawarar kudin goron da aka yi wa bakin haure, kuma ta tsaya a matsayinta na bayar da shugabanci da kyakkyawan fata a lokacin da ake cikin wani yanayi na rashin tabbas da rikice-rikice a duniya.