Za a yi bincike kan labaran 'kanzon kurege'

Amurka
Bayanan hoto,

An yi ta samun labaran kanzon kurege lokacin zaben shugaban kasar Amurka Donald Trump

'Yan majalisar dokokin Birtaniya sun kaddamar da wani bincike kan yadda ake samun karuwar labaran kanzon kurege.

Kwamitin Al'adu da yada labarai da kuma wasanni na majalisar ya ce zai duba yadda ake dauke hankalin mutane da labaran da ba na gaskiya ba.

Binciken zai yi duba a kan majiyoyin labaran kanzon kurege da yadda suke yaduwa da kuma tasirinsu a kan dimokradiyya.

Kwamitin ya ce zai gudanar da wannan bincike ne saboda korafin da masu kada kuri'a a Amurka suka yi kan yadda yada labaran karya ya yi tasiri a zaben shugaban kasa.

Shugaban kwamnitin, Damian Collins, ya ce karuwar furofaganda da ƙirƙiro da labaran karya "wata barazana ce ga mulkin demokradiyya kuma yana rage amincewar da ake da ita kan kafofin yada labarai baki daya''.