Nigeria ta ce ba za ta lamince a rusa gine-ginen tunawa da bauta ba

Najiriya

Asalin hoton, Government of Nigeria

Bayanan hoto,

Ministan ya yi alkawali za a yanke wa wadanda suka rusa ginin hukunci

Ministan Yada Labarai da Al'adu na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya ce gwamnatin kasar ba za ta lamunce wa rusa gine-ginen tunawa da bauta ba.

Ministan ya tabbatar da hakan ne a lokacin da ya ziyarci inda wani ginin tunawa da bauta ya kasance a Legas, babban birnin kasuwancin kasar.

Wadansu 'yan kwangila masu zaman kansu ne dai suka rusa ginin mai salon gine-ginen Brazil wanda bayin da suka dawo gida suka gina shekara 190 da ta gabata.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa-hannun mai ba shi shawara a kan lamuran yada labarai Segun Adeyemi, ministan ya ce gwamnati za ta garzaya kotu don sake mallakar wurin da nufin sake tayar da ginin.

''Wannan kamar wani abu ne da ke tuna mana tarihinmu. Yana kuma nuna salon gine-ginen Brazil a wancan lokacin, wadanda da wuya a samu irin su a duniya''.

Ya kuma kara da cewa, ''[Ginin] yana kuma tuna mana irin bakar wahalar da kakannin kakanninmu suka sha a lokacin bauta da kuma yadda suka yi nasara, har suka dawo gida suka nuna irin wadatar da Allah Ya yi masu".