Ana so a hana Trump shiga Birtaniya

May and Trump
Bayanan hoto,

Theresa May ta ki sauraron korafi kan dakatar da ziyarar Trump

Wata takardar koke da aka gabatar don kokarin hana shugaban Amurka Donald Trump shiga Birtaniya, ta samu sa hannun fiye da mutum miliyan daya.

Yawan mutanen da ke sanya hannu a takardar na karuwa sosai tun bayan da Amurka ta dauki wasu matakai na hana 'yan wasu kasashe shiga kasarta.

Firai ministar Birtaniya Theresa May ce ta sanar da ziyarar tasa lokacin da ta ziyarci Amurka a makon da ya gabata.

Sai dai gwamnatin Birtaniyar ta yi watsi da kiran da ake mata na soke ziyarar.

Shugaban jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn, ya nemi Firai ministar da ta dage ziyarar zuwa wani lokaci a gaba.

Yanzu haka takardar koken ita ce kan gaba a shafin intanet na gwamnatin Birtaniyan.

Takardar na cewa, ''Za a kyale Donald Trump ya shiga Birtaniya a matsayinsa na shugaban Amurka, amma kuma kar a kira zuwan nasa da sunan ziyarar aiki, don hakan zai jawo wa sarauniyar Ingila abin kunya.''

Firai minista Theresa May za ta tattauna batun a ranar Talata.

Tun bayan da shugaba Donald Trump ya sanya hannu kan dokar hana wasu kasashen Musulmai bakwai Amurka da kuma kin karbar bakuncin 'yan gudun hijira Musulmai, yake ta shan suka daga bangarori daban-daban na duniya.

Al'amarin ya jawo har dubban Amurkawa suka fito zanga-zangar kin amincewa da matakin nasa.

Amma duk da wannan ce-ce-ku-ce Mista Trump ya ce yana nan a kan bakansa ba komawa baya.