West Ham ta ce Payet bai yi 'halacci ba'

Dmitry Payet

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Payet bai sake buga wa West Ham wasa ba tun lokacin da Manchester City ta lallasa ta da ci 5-0

West Ham ta ce Dimitri Payet ya yi rashin "halacci kuma bai yi mutunci ba" da ya sake koma wa Marseille a kan fam miliyan 25.

Kulob ɗIn ya dage a kan cewa babu buƙatar sayar da Payet kuma shugaban ƙungiyar David Sullivan, ya ce yana son ɗan wasan ya ci gaba da zama don ya zama "abin misali."

Sai dai kocin ƙungiyar, Slaven Bilic ya amince da cinikin Payet bisa "muradin tabbatar da haɗin kan ƙungiyar".

Ɗan wasan tsakiyar ya shiga West Ham ne a watan Yunin 2015 daga Marseille kuma ya sabunta kwantiraginsa da shekara biyar da rabi kafin ya sa hannu a kan yarjejeniyar koma wa Marseille tsawon shekara huɗu da rabi.

Ya yi fice a kakarsa ta farko a West Ham, inda ya ci ƙwallo 12 kuma an gabatar da sunansa a jerin 'yan wasan da za a zaɓa gwarzon shekara.