Trump ya sauke matar da ta 'hana' shi korar Musulmi

Masu zanga-zanga sun mamaye filin jirgin saman JFK

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanga sun mamaye filin jirgin saman JFK

Shugaban Amurka Donald Trump ya kori Antoni Janar din kasar ta rikon-kwarya Sally Yates bayan ta ki goyon bayan shirinsa na korar 'yan gudun hijira da Musulmi daga kasar.

Wata sanarwa da fadar White House ta fitar ta ce Ms Yates ta "yaudari" ma'aikatar shair'ar kasar.

Antoni Janar din gundumar Gabashin Virginia, Dana Boente ne zai maye gurbinta.

Antoni Janar din Amurka ta rikon-kwarya ta shaida wa ma'aikatar shari'ar kasar kada ta kare shirin Shugaba Donald Trump na korar 'yan gudun hijira da Musulmi daga kasar.

Sally Yates, wacce tsohon shugaban kasar Barack Obama ya nada a kan mukamin, ta ce ba ta "gamsu" da halascin shirin shugaban na korar Musulmi ba.

Ta kara da cewa, "Idan dai ni ce zan ci gaba da zama a kan wannan mukamin, ba za a aiwatar da shirin ba".

Amma fadar White House ta ce Ms Yates ta "ta yaudari ma'aikatar shair'a saboda ta ki tabbatar da doar da aka yi domin kare Amurkawa".

Sanarwar da kakakin shugaban kasar ya sanya wa hannu ta kara da cewa "Shugaba Trump ya sauke Ms Yates daga kan mukaminta".

Hanin da Mr Trump ya yi wa 'yan kasashe bakwai na Musulmi daga shiga Amurka ya janyo gagarumar zanga-zanga a Amurka da wasu kasashe.

Mr Trump ya zargi jam'iyyar Democratic Party da yin kafar-ungulu a yunkurinsa na kafa gwamnati domin kawai "dalilai na siyasa".

'Jakadu sun bi sahu'

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da daruruwan jakadun Amurka a wasu kasashe suka amince da murya daya su soki shirin na Mr Trump.

Sun ce hana Musulmi shiga kasar ba zai sa ta zauna lafiya ba, suna masu cewa hakan ya saba da ka'idojin Amurka kuma zai aike da sako maras dadi ga kasashen Musulmi.

Haramcin shiga Amurka ya shafi 'yan kasashen Iraq, Syria, Iran, Libya, Somalia, Sudan da kuma Yemen.

Tuni dai masu rajin kare hakkin dan adam da 'yan gudun hijira suka kalubalancin shirin na Mr Trump a gaban kuliya.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Sally Yates ta ce ba za ta bari a keta doka ba

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan uwan wasu da lamarin ya shafa

Ms Yates mataimakiyar antoni janar Loretta Lynch ce lokacin shugabancin Obama. Ta zama antoni janar ta rikon-kwarya bayan Ms Lynch ta sauka daga mukamin.

Shugaba Trump din ne ya bukaci ta ci gaba da rike mukamin har sai 'yan majalisar dattawa sun amince da mutumin da yake son nadawa domin maye gurbinta.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanga a birnin London