Maganin Maleriya ya kasa aiki a Birtaniya

Cutar cizon sauro

Asalin hoton, SPL

Bayanan hoto,

An kamuwa da cutar cizon sauro daga cizon sauro mai miyagun kwayoyin

Likitoci a Birtaniya sun ce a karon farko maganin maleriya ya ki ya yi tasiri bayan an bai wa marasa lafiya a Birtaniya.

Hade-haden maganin ya ki ya warkar da marasa lafiya hudu, wadanda suka ziyarci Afrika, bayan alamu alamun farko sun nuna cewa kwayoyin cutar na bijirewa magunguna.

Wata tawaga a makarantar nazarin tsafta ta London ta ce bai kamata a yi gaggawar daga hankali ba.

Amma ta yi gargadi cewa al'amura na iya dagulewa don haka ta bukaci a yi gaggawar gano maganin da ke tasiri kan cutar a Afirka.

Cutar maleriya na yaduwa ne idab sauro mai dauke da kwayar cutar ya ciji mutum.

Tsakanin mutam 1,500 da 2,000 aka warkar daga cutar maleriya a Birtaniya a shekarar da ta gabata - a duk lokacin da suka yi tafiya.

Da yawansu sun warke ne bayan shan maganin maleriya da aka hada da sinadaran artemether-lumefantrine.

Cutar maleriya dai ta fi kamari a kasashen Afirka, inda har ake samun yawan mace-mace sakamakonta.