Jamus: Wasu matasa 6 sun mutu a wajen liyafa

Asalin hoton, AFP
'Yan sanda na bincike a lambun da lamarin ya faru
An gano gawawwakin wasu matasa shida a wajen da su ka yi wata 'yar kwarya-kwaryar liyafa (party) a kasar Jamus.
'Yan sanda sun ce ba a san dalilin mutuwar tasu ba, kuma ba bu wani alamun fada ko rauni a jikinsu.
Daya daga cikin labarin da ake yadawa game da mutuwar matasan - wadanda shekarunsu ba su wuce 18 zuwa 19 ba shi ne, sun mutu ne sanadiyyar shakar gurbatacciyar iska bayan sun hura wuta domin su sha dumi.
Wannan lamari dai ya faru ne a garin Bavarian, kuma mahaifin biyu daga cikin matasan ne ya gano gawawwakin a lambun gidansa inda suka yi liyafar.
Tuni dai an kaddamar da wani bincike na gano miyagun laifuka da kuma na asibiti don a gano musabbabin mutuwar matasan.