'Yan sandan Jamus sun tilasta wa wata mata tatso ruwan Nononta

Gayathiri Bose

Asalin hoton, GAYATHIRI BOSE

Bayanan hoto,

Jami'an sun tilastawa Bose ta bude rigarta don ta tabbatar musu cewa tana shayarwa

Wata mata ta kai karar 'yan sandan Jamus saboda jami'an sun tilasta mata ta tatso ruwan nononta a wani wurin binciken mutane a filin jiragen sama da ke Frankfurt.

An tilasta wa matar ta yi hakan ne domin ta tabbatar wa da mahukunta cewa tana shayarwa.

Gayathiri Bose ta shaida wa BBC cewar lamarin ya sa ta matukar jin kunya kuma za ta kai kara kotu.

Ta kara da cewa 'yan sandan da ke aiki a filin jirgin sun yi zarginta saboda tana dauke da na'urar da ake tatsar ruwan nono, amma ba ta tare da ɗan da ta ke shayarwa.

'Yan sandan Jamus dai sun ki su yi magana da BBC a kan zargin da ake yi musu.

Amma sun ce wannan ba abu ne da suka saba yi ba a aikin binciken da suke yi kullum.

Ina jaririnki?

Misis Bose, wacce ita kadai ce ta ke bulaguro a lokacin da lamarin ya faru , ta ce tana hanyarta ta zuwa birnin Paris ne a a ranar Alhamis din makon da ya gabata, sai aka tsayar da ita a wajen da ake binciken mutane.

Matar 'yar kasar singapore mai shekara 33 ta ce, "Bayan jakata da ke dauke da na'urar tatsar ruwan nono ta wuce ta cikin na'urar da ke binciken jakukuna a filin jirgin, sai aka kai ni gefe guda aka fara yi min tambayoyi".

Ta ce, "Sun yi min tambayoyi a fusace. Kina shayarwa? Ina jaririnki? Jaririnki na Singapore?"

Misis Bose ta ce ta fuskanci cewa jami'an ba su amince da ita ba da ta shaida musu cewa na'urar tatsar ruwan nono ne.

Jami'an sun kuma rike mata fasfonta sai wata jami'a ta raka ta wani daki inda aka ci gaba da yi mata wasu tambayoyi.

A cikin dakin ne jami'ar ta ce sai ta tabbatar mata cewa tana shayarwa.

Ta kara da cewa, "Ta ce na bude rigata na nuna mata nonona. Sai ta ke tambaya ta me yasa bata ga komai a makale a kan nonon ba, idan dai har da gaske ina tatsar ruwan mama".

"Sai na ce mata ai ba a makale yake a jikin nono ba a ko da yaushe, dama makalawa muke yi a jikin maman a lokacin da muke bukatar tatsar ruwan sai na'urar ta tatso.

Asalin hoton, GAYATHIRI BOSE

Bayanan hoto,

Jami'an tsaro sun yi zargin na'urar tatsar ruwan nonon Bose

Misis Bose ta ce "Na tatso kadan, na kadu matuka. Ni kadai ce a lokacin kuma ina ta tunanin ko me zai biyo bayan hakan idan har suka cuzguna min.''

Ms Bose ta ce jami'an sun gwada na'urar sannan daga bisani suka dawo mata da fasfonta kuma suka kyale ta ta hau jirginta zuwa Paris. Ms Bose ta tambayi sunan jami'ar kuma ta rubuta a kan wata takarda.

Abin rikitarwa

Misis Bose ta ce lamarin, wanda ya dauki tsawon minti 45, ya sa ta ji kunya kuma ya matukar rikitar da ita.

"Bayan sun kammala bincikensu, sai na gaya musu cewa bai dace su rika yi wa mutane haka ba. Na ce ko kun san kuwa abin da kuka yi, kun sa ni na nuna muku nonona"?

"Sai jami'ar ta ce , 'to yanzu dai ya wuce sai ki tafi'. Bata damu ba kwata kwata. Ba ta ma nuna alamun da nasanin abin da ta aikata ba.''

Tuni dai Bose ta shigar da kara kan lamarin.