Austria ta haramta wa mata fita waje da burka

Wata mata da burka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kasashen Turai da dama suna hana saka burka wasu kuma suna duba yiwuwar halasta shi

Gwamnatin hadin gwiwar Austria ta amince ta hana mata saka burka a wurin taruwar jama'a kamar makarantu da kotuna.

Kasar tana kuma duba yiwuwar hana ma'aikatan kasar saka dankwali da wasu tufafi masu alaƙa da addini.

Ana ganin wannan shawara a matsayin wani yunƙurin daƙile 'yancin da jam'iyyar masu ra'ayin rikau, wanda dan takararsu ya sha kaye da kyar a zaben shugaban kasar na watan da ya gabata ke ci gaba da samu.

A makon da ya gabata ne gamayyar jam'iyyu masu matsakaicin ra'ayi suka kusa rugujewa sakamakon wani rikici a kan wata yarjejeniya game da makomar gwamnatin.