Su wa makami mai linzamin Iran ke wa barazana?

Ballistic Missile

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shirin Iran na sarrafa makamashin nukiliya wanda ta sha cewa na zaman lafiya ne ya haifar da fargaba a zukatan ƙasashe

Gwajin makami mai linzamin da Iran ta yi a baya-bayan nan ya bar baya da ƙura, inda wasu ƙasashe ke kallon matakin a matsayin tsabagen keta ƙudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Iran ta yi irin waɗannan gwaje-gwaje da dama tun bayan ƙulla yarjejeniyar nukiliya ta 2015, wadda ta kai ga sassauta wa ƙasar takunkumai.

Ba a dai iya tantancewa ƙarara nau'in makamin da Iran ɗin ta harba ba, ko abin da ta yi ya saɓa da tanade-tanaden Majalisar Ɗinkin Duniya.

Firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce zai bijiro da batun sake ƙaƙaba wa Iran takunkumai yayin ganawarsa da shugaban Amurka Donald Trump a watan Fabrairu.

An dakatar da wani ƙuduri na 2010 da ke hana Iran gudanar da duk wani aiki kan "makamai masu linzami da ke iya ɗaukar nukiliya", bayan yarjejeniyar nukiliyar da manyan ƙasashen duniya shida suka ƙulla da ita.

An maye gurbinsa da wani sabon ƙuduri na 2231 da ke cewa "kada Iran ta yi duk wani abu mai alaƙa da ƙera makami mai linzamin da zai iya safarar nukiliya".

Su wane ne ba sa son Iran ta yi gwaji?

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani taro ranar Talata a kan gwajin makami mai linzamin na Iran, kamar yadda Amurka ta buƙata.

Shi ma a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Benjamin Netanyahu ya ce "Sai Iran ta yi bayani a kan wannan takalar faɗa".

Firai ministan na Isra'ila babban mai sukar yarjejeniyar nukiliyar da aka ƙulla da Iran ne, ƙasar da ke rajin a shafe Isra'ila daga banƙasa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wani sojan rundunar juyin-juya-hali a kusa da abin harba makami mai linzami a wani waje da ba a bayyana ba a shekara ta 2016

Wakilin BBC a kan harkokin diflomasiyya a Tel viv, Jonathan Marcus, ya ce matakin Mista Netanyahu na yin tir da gwajin wata manufa ce ƙarara ta matsa lamba ga sabuwar gwamnatin Donald Trump don ta ɗauki mataki a kan hukumomin kasar ta Iran.

Haka zalika, gwajin makamin zai ƙara haddasa zaman ɗar-ɗar tsakanin Iran da Saudiyya, manyan ƙasashen yankin Gulf masu bambancin ɗariƙa da ke yunƙurin faɗaɗa tasirinsu a tsakanin ƙasashen yankin.

Ita dai Iran ta dage a kan cewa tun da dai ba ta da shirin sarrafa makaman nukiliya, ba a haramta muta gwaje-gwaje ba.

Gwajin da Iran ta yi ka iya tilasta Donald Trump fito da wani jadawali ƙarara da zai fayyace matakan da Amurka za ta ɗauka a kanta.

Makomar yarjejeniyar nukiliya ta Iran

Da aka tambaye shi yayin wani taron manema labarai a ranar Talata, Ministan Wajen Iran Mohammad Javad Zarif cewa ya yi kawai, "Gwajin makami mai linzami ba ya cikin yarjejeniyar nukiliya da aka cimma".

Iran ta ce shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne tsantsa, sai dai manyan ƙasashen duniya na zargin ta da ƙoƙarin ƙera makamai masu linzami.

Fadar White House ta ce tana nazarin wannan al'amari a yanzu.

Sai dai Sanata Bob Corker, shugaban kwamitin hulɗa da ƙasashen waje a majalisar dattawan Amurka, ya ce: "Ba za a lamunta Iran ta ci gaba da keta dokokin gwajin makami mai linzami ba."

A baya Donald Trump ya ce yarjejeniyar nukiliyar Iran "wata masifa ce" kuma ya nuna cewa gwamnatinsa za ta yi watsi da ita.

Tsohon shugaban hukumar leƙen asirin Amurka, CIA, John Brennan, wanda ya sauka bayan rantsar da Donald Trump, ya faɗa wa BBC a bara cewa yin watsi da yarjejeniyar nukiliyar Iran "tsagwaron wauta ce" kuma "annoba".

Sai dai sabon shugaban hukumar Mike Pompeo, wanda ya gaji John Brennan, shi ma babban mai sukar lamirin yarjejeniyar nukiliyar ne.