'Suarez ne dan wasan da ya fi tagomashi a watan Janairu'

Luis Suarez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Suarez ne dan wasan PFA na shekarar 2013/14

Mabiya labaran wasanni na BBC sun ce dan wasan Liverpool Luis Suarez shi ne dan kwallon da ya fi kowanne tagomashi cikin wadanda aka yi musayarsu a kasuwar saye da sayar da 'yan wasa a watan Janairu.

mun tambayi mabiya labaran wasanni su fadi 'yan wasa goma da suke gani sun fi tagomashi a lokacin musayar 'yan kwallo, kuma kashi 61 sun zabi Suarez.

Dan kasar ta Uruguay ya koma Anfield a shekarar 2011 a kan £22.7m sannan ya zura kwallo 82 a wasanni 133 da ya buga, kafin ya koma Barcelona a kan £75m a shekarar 2014.

Dan wasan Manchester United Nemanja Vidic shi ne ya zo na biyu inda ya samu kashi 26, yayin da abokinsa Patrice Evra ya zo na uku bayan ya samu kashi uku na kuri'un da kuka kada.

'Yan wasan biyu sun koma Old Trafford ne a shekarar 2006 inda suka taimakawa kulob din ya lashe kofin gasar Premier biyar da kuma na zakarun Turai daya.

Dan wasan Liverpool Daniel Sturridge ne ya zo na hudu, yayin da dan wasan baya na Chelsea Gary Cahill ya zo na biyar.