Wayne Rooney ba zai bar Man Utd ba — Jose Mourinho

Wayne Rooney

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wayne Rooney ya zura wa Manchester United kwallo 250

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce kyaftin Wayne Rooney ba zai bar kulob din a kakar wasa ta bana ba.

A ranar 21 ga watan Janairu ne dan wasan mai shekara 31 ya kafa tarihin na dan kwallon da ya fi zura wa kulob din wasa a karawar da suka yi da Stoke sannan ya buga wasa na 28 a kakar wasa ta bana a wasan cin kofin FA da suka yi da Wigan ranar Lahadi.

An yi ta rade-radin cewa Rooney na shirin komawa China.

Mourinho ya kara da cewa shi ma Ashley Young zai ci gaba da zama a Old Trafford.

Bayana nasarar da suka yi ranar Lahadi ne, Mourinho ya ce Young shi ne dan wasan da kadai zai iya barin kulob din a watan nan.

Kocin na United ya zabi Rooney domin ya buga karawar da za su yi da Hull a gasar Premier ranar Laraba.

Mourinho ya ce, "An gama komai, don hana Young zai ci gaba da zama da ni har karshen kakar wasa ta bana."