Odion Ighalo ya koma kulob din China kan £20m

Odion Ighalo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kwallo daya kacal Odion Ighalo ya zura a kakar wasa ta bana

Kulob din Watford ya sayar da dan wasan Nigeria Odion Ighalo ga kulob din Changchun Yatai na kasar China a kan £20m.

Ighalo, mai shekara 27, ya koma Watford ne a shekarar 2014 daga kulob din Udinese kuma ya taimakawa Watford ya kai matsayin shiga gasar Premier a kakar wasanni ta 2014-15.

Ya zura kwallaye masu armashi 15 a kakar wasa ta 2015-16, amma kwallo daya kacal ya zura a gasar Premier ta bana, inda ya buga wasanni 15 a jere ba tare da zura kwallo ko daya ba.

Watford na mataki na 14 a tebirin gasar Premier, kuma maki takwas ya rage a fitar da ita daga gasar.

Lokacin da yake buga wasanni a Watford, Ighalo ya doka wasanni 100 a gasa daban-daban da kulob din ya shiga, inda ya ci kwallo 39.