Kun taba ganin yarinyar da bishiya ke tsiro a jikinta?

Sahana Khatun

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Likitoci na fatan Sahana Khatun, mai shekara 10, ba za ta samu gagarumar matsala ba

Lokacin da wani tsiro mai kama da ɓawon bishiya ya fara bayyana a fuskar wata yarinya 'yar shekara 10 Sahana Khatun wata huɗu da ya wuce, mahaifinta bai damu ba.

Sai dai bayan sun fara yaɗo, ya damu matuƙa, inda ya tafi kudu da ƙauyensu zuwa Dhaka babban birnin Bangladesh don neman magani.

Yanzu likitoci na fargabar cewa Sahana ka iya zama mace ta farko da ta taɓa fuskantar abin da ake kira "larurar tsirowar bishiya a jiki".

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A bara warhaka Abul Bajandar ya yi fama da irin wannan matsala, amma yanzu ya warke

Idan gwajin da suka yi ya tabbata, yarinyar ta shiga rukunin wasu mutane 'yan ƙalilan a faɗin duniya da ke fama da wannan larura mai suna epidermodysplasia verruciformis.

Wasu mutane ƙalilan - duka maza ne- ake tsammanin suna da wannan cuta.

Ga wasu mutanen, har ta ci ƙarfinsu, inda wani mutum ba ma ya iya taɓa mata da ɗansa tsawon shekara goma kenan.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mahaifin Sahana, Mohammad Shahjahan na fatan lokitoci za su taimaki 'yarsa

Hannuwan Abul Bajandar duk wani tsiro ya fito musu inda suka yi girman kilogram biyar, ga kuma wani tofo a ƙafafuwansa, idan ka gan shi tamkar bishiya.

Mutumin mai shekara 27, shi ne ɗan ƙasar Bangaladesh na farko da aka gano na ɗauke da cutar kuma a yanzu an yi masa aiki har sau 16 a asibitin kwalejin koyon aikin likitanci ta Dhaka don samun damar ci gaba da amfani da hannunsa.

Likitoci na fatan cewa larurar Sahana ba irin azababbiyar nan ba ce, don haka tana iya samun sauƙi cikin hanzari.

Mahaifin Sahana, Mohammad Shahjahan ya ce "Mu talakawa ne. 'Yata ta rasa mahaifiyarta tun tana 'yar shekara shida. Ina da kyakkyawan fatan cewa likitoci za su sassaƙe ɓawon bishiyar da ke fitowa a kyakkyawar fuskar 'yata."