Trump ya nada Neil Gorsuch a matsayin alkalin kotun koli

Neil Gorsuch (tsakiya) da matarsa Marie Louise lokacin da Donald Trump ya nada shi

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Neil Gorsuch (tsakiya) da matarsa Marie Louise lokacin da Donald Trump ya nada shi

Shugaban Amurka Donald Trump ya nada alkalin kotun daukaka kara ta tarayya da ke jihar Colorado Neil Gorsuch a matsayin alkalin kotun kolin kasar.

Idan aka tabbatar da shi, dan shekara 49 din, zai cike gibin da aka samu a kotun kolin tun bayan mutuwar mai shari'a Antonin Scalia.

Dole ne dai majalisar dattawa ta amince da shi kafin a tabbatar masa da mukamin, amma shugaban 'yan majalisar na bangaren jam'iyyar Democrat ya ce yana da matukar "shakku kan" Gorsuch.

Kotun kolin ce ke yanke hukunci a kan manyan batutuwan da suka shafi rayuwar Amurkawa, cikin su har da batun zubar da ciki da rike bindiga.

Mr Trump ya ce alkali Gorsuch yana da "matukar basira da ilimin shari'a da kuma iya fassara kundin tsarin mulki".

An gudanar da zanga-zanga a wajen kotun koli domin nuna adawa da nadin da Mr Trump ya yi wa alkali Gorsuch.

Da yake amincewa da nadin nasa, Gorsuch ya bayyana marigayi, wanda ya mutu a shekarar da ta wuce, a matsayin "gwarzo a fannin shari'a".

Ya kara da cewa, "Na yi matukar farin ciki da kuma nuna kankan da kai saboda wannan nadi".

An zabe shi ne a cikin alkalai 21 da aka mika wa Mr Trump sunayensu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mai shari'a Scalia (na biyu daga gaba) na daya daga cikin alakai biyar masu tsattsauran ra'ayi