Sanatocin Democrat sun yi wa Trump bore

'Yan jam'iyyar Democrats sun ce suna bukatar karin bayani a kan Tom Price da Stephen Mnuchin

Asalin hoton, Reuters da Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan jam'iyyar Democrats sun ce suna bukatar karin bayani a kan Tom Price da Stephen Mnuchin

'Yan jam'iyyar Democrats na Kwamitin Harkokin Kudi a Majalisar Dattawan Amurka sun kaurace wa zaman kada kuri'ar tabbatar da wasu mutum biyu da Donald Trump ke shirin bai wa mukamai.

Wannan mataki ya sa ala tilas aka dage zaman kada kuri'ar.

Sun ce suna bukatar karin bayani game da harkokin kudin Tom Price - wanda aka gabatar da sunansa a matsayin wanda zai kula da Ma'aikatar Lafiya da kuma Stephen Mnuchin - wanda aka gabatar da sunansa a matsayin wanda zai kula da Baitul Malin kasar.

Haka kuma an dage kada kuri'ar tabbatar da wanda aka gabatar da sunansa a matsayin antoni janar Jeff Sessions.

A ranar Litinin ne shugaban kasar ya kori mai rikon mukamin antoni janar din kasar bayan da ta kalubalanci umarnin da ya bayar na hana wasu musulmai shiga kasar.

Umarnin dai ya dakatar da 'yan wasu kasashen musulmai bakwai shiga kasar na wucin gadi.

'Yan kwamitin kula da harkokin kudaden na jam'iyyar Democrats sun shaida wa manema labarai cewa suna neman karin bayani game da harkokin kudaden Tom Price.

An zabi dan majalisar dokoki da ke wakiltar Georgia a matsayin sakataren harkokin lafiya da na ayyukan jinkai a sabuwar gwamnatin.

Sanatocin sun ce sun damu game da rahotannin da suke samu game da halayyar Stephen Mnuchin a wani tsohon bankinsa.

'Yan jam'iyyar democrats na kwamitin harkokin kudi a majalisar dattawan Amurka na kauracewa zaman kada kuri'ar tabbatar da wasu mutane biyu da Donald Trump ke shirin bawa wasu muhimman mukamai biyu a gwamnatinsa yanayin da ya sa ala tilas aka dage zaman kada kuri'ar.