Kasashen Afirka za su fice daga kotun manyan laifuka ta ICC

ICC

Asalin hoton, ICC

Bayanan hoto,

Tun a 2002 ne kotun ta ICC ta shiga cikin harkokin shari'a na duniya, sai dai Afirka na ganin ana nuna son kai

Tarayyar Afirka ta mara wa wani shiri baya na matsa lamba don janyewar ƙasashen nahiyar gaba ɗaya daga Kotun Hukunta Laifukan yaƙi ta Kuniya (ICC), wadda suka ce ba ta yi musu adalci.

Shawarar wadda ƙungiyar ta cimma a wani zaman sirri yayin taron ƙolin tarayyar Afirka, bai zama wajibi kowacce ƙasa ta yi biyayya da shi ba.

Jagororin Afirka sun ce tuhumar shugabannin ƙasashe kamar Omar al-Bashir na Sudan kan aika-aikar da aka tafka a Darfur da takwaransa Uhuru Kenyatta na Kenya kan tunzura rikicin bayan zaɓen ƙasar, ya nuna cewa kotun ta sauka daga kan alƙibla.

Shirin Tarayyar Afirkan ya ba da shawarar cewa ƙasashen nahiyar su inganta harkokin shari'arsu sannan a faɗaɗa hurumin kotun hukunta manyan laifuka da take haƙƙoƙin ɗan'adam ta Afirka.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Nijeriya na daga cikin ƙasashen Afirka da ke da ra'ayin nahiyar ta ci gaba da zama a kotun hukunta manyan laifuka

Akwai dai rarrabuwar kawuna a tsakanin ƙasashen Afirka kan matakin janyewa daga kotun saboda yadda ta fi haƙon shugabannin nahiyar wajen tuhumarsu kan laifuka.

Ƙasashe irinsu Nijeriya na ganin fita daga ICC ba zai zame wa Afirka alheri ba.

Yayin da Kenya da Uganda da Sudan waɗanda kotun ke tuhumar wasu shugabanninsu ke matsa ƙaimi don ganin Afirka ta janye jiki.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi Allah-wadai da matakin da wasu kasashe irinsu Gambia suka dauka a baya na fice wa daga kotun ta ICC.