Kasuwar 'yan wasa ta yi kyau ga ƙungiyoyin Premier

Premier League
Bayanan hoto,

Odion Ighalo, Robbie Brady, Manolo Giabbiadini da Mamadou Sakho na daga cinikin ƙarshe-ƙarshe da aka yi musayar Janairu

Ƙungiyoyin ƙwallon Premier ta Ingila sun ci riba karon farko a kasuwar musayar 'yan wasa - inda suka yi cinikin fam miliyan 215, rabon da su samu maƙudan kuɗi kamar haka shekara shida kenan.

Southampton da Burnley su ne suka rufe hada-hada a kasuwar, yayin da Odion Ighalo ya koma China daga Watford a kan kuɗi fam miliyan 20.

Southampton ta sayo Manolo Gabbiadini daga Napoli a kan kimanin fam miliyan 14, Burnley ta ɗauko Robbie Brady a kan sama da fam miliyan 13.

Manyan ƙungiyoyin Premier sun samu ribar fam miliyan 40 idan an kwatanta da kuɗin da suka kashe wajen sayen 'yan wasa a cewar mujallar Deloitte mai sharhi kan harkokin kuɗi.

Ƙungiyoyin Premier sun kashe kimanin fam biliyan daya da miliyan 38 wajen sayen 'yan wasa a bana, bayan sun kashe fam biliyan daya da miliyan 165 da bazara.

Kuɗin da aka kashe a Janairun 2017 shi ne na biyu mafi yawa - a kan fam miliyan 225 a shekara shida da ta wuce.

Bayanan hoto,

Alƙaluman bayani a kan 'yan wasan da suka fi tsada a musayar Janairu da aka rufe

Babban cinikin da aka yi a ranar ƙarshe ta musayar shi ne ɗan ƙwallon gaban Nijeriya Ighalo mai shekara 27, wanda ya koma ƙungiyar Changchun Yatai a China.

Burnley ne kulob ɗIn da ya fi hada-hada, inda ya ɗauko Brady mai shekara 25 daga ƙungiyar Norwich bayan tun da farko sun zari wani ɗan wasan tsakiya, Ashley Westwood, daga Aston Villa.

Southampton ta ƙara ƙarfin gabanta inda ta ɗauko Gabbiadini, ɗan shekara 25, yayin da Crystal Palace ta samu aron ɗan bayan Liverpool Mamadou Sakho kuma ta sayo Luka Milivojevic daga Olympiakos na Girka.

Swansea City ta ɗauko ɗan wasan gaban Aston Villa, Jordan Ayew a wata musaya da ta bai wa Neil Taylor damar koma wa Villa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Oscar shi ne ɗan wasan da Chelsea takarɓi maƙudan kuɗi bayan ta sallama wa wata ƙungiya a China

Ciniki bai faɗa ba tsakanin Celtic da Chelsea, inda golan Celtic Craig Gordon da ɗan wasanta na gaba Moussa Dembele suka ci gaba da zamansu a Scotland.

Everton ce ta fi kashe maƙudan kuɗi a kan wani ɗan wasa, inda ta biya Manchester United fam miliyan 22 don sayen ɗan wasan tsakiyar Faransa Morgan Schneiderlin.

Chelsea ce ta fi kwasar kuɗi har fam miliyan 60 daga ƙungiyar Shanghai SIPG ta China bayan ta sayar da Oscar.

Daga cikin waɗanda suka bar Premier akwai Dmitri Payet - wanda West Ham ta zarga da rashin "mutunci da halacci" bayan ya sake koma wa Marseille a kan fam miliyan 25.

Ba a ji amon manyan ƙungiyoyin Premier shida ba a musayar Janairun da aka rufe - sabuwar sayayyar da aka ji ita ce wadda Arsenal ta yi inda ta ɗauko ɗan wasan gefen hagu Cohen Bramall a kan fam dubu 40.