Ɗan duba ya yi wa shugaban ƙasa ƙaryar mutuwa

Sri Lanka

Asalin hoton, ISHARA S.KODIKARA

Bayanan hoto,

Malamin duban yanzu ya ce shugaban Sri Lanka zai mutu a watan Oktoba

'Yan sanda sun kama wani ɗan duba wanda ya yi hasashen cewa shugaban ƙasar Sri Lanka, Maithripala Sirisena zai mutu a watan jiya, ko da yake har yanzu bai mutu ba.

Vijitha Rohana Wijemuni wanda ya taɓa aiki a rundunar sojan ƙasar, ya wallafa bidiyo a shafin sada zumunta, inda ya ce shugaba Sirisena zai gamu da wani mummuna hatsari ko wata cutar ajali ranar 27 ga watan Janairu.

Daga bisani, malamin duban ya ɗaga mutuwar shugaban ƙasar zuwa watan Oktoba.

Masu shigar da ƙara sun ce iƙirarin dubo ranar mutuwar shugaban ƙasa, wani jafa'i ne ko ɓata suna.

An taɓa ɗaure wani fitaccen ɗan duba a Sri Lanka a gidan yari na wani taƙaitaccen lokaci, shekara 30 da ta wuce bayan ya ci zarafin Rajiv Gandhi, wanda shi ne Fira ministan Indiya a lokacin.