Nigeria na nazari don ba 'yan ƙasar ikon yin zaɓe a waje

INEC

Asalin hoton, Channels TV

Bayanan hoto,

Wasu ƙungiyoyin 'yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje sun yi ta kiraye-kiraye a baya don a ba su damar jefa ƙuri'a

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Nijeriya ta kafa wasu kwamitoci ciki har da wanda zai yi nazari don bai wa 'yan ƙasar mazauna ƙetare damar kaɗa ƙuri'unsu a zaɓukan ƙasar.

Kwamitin mai wakilai 10 a ƙarƙashin wata kwamishiniyar hukumar, Hajiya Amina Zakari, na da makonni shida don miƙa rahotonsa.

Sharuɗɗan aikin kwamitin sun haɗa da ƙididdige yawan 'yan Najeriya da yaɗuwarsu, da kuma wuraren da suke zaune a ƙasashen waje.

Kwamitin zai kuma yi nazari a kan tsarin doka da na siyasa da na zaɓe da za a yi la'akari da su wajen tsara shirin kaɗa ƙuri'a daga ƙasashen waje.

Baya ga wannan kwamiti, hukumar ta kuma kafa kwamiti a kan bitar mazaɓun ƙasar da kuma mazaɓun da 'yan majalisa ke wakilta da kwamitin bitar cibiyar tattara bayanan taswirar ƙasa.