Za a ɓullo da dokar zauna-ka-hutu a ƙwallon ƙafa

SIN-BINS

Asalin hoton, Nasidi Yahaya

Bayanan hoto,

Za a fara amfani da sabuwar ce a ƙananan gasa kafin ta kai manyan gasar ƙwallon ƙafa

A watan gobe dokar zauna-ka-huta ga 'yan wasan da suka yi laifi kuma aka ba su yalon kati a wasannin ƙwallon ƙafa ka iya fara aiki.

Hukumar tsara dokokin ƙwallon ƙafa ta duniya IFAB ce za ta yi nazari kan ƙudurin yayin taronta na bana a London cikin watan Maris.

An fara jarraba matakin a rukunonin gasar Turai a 'yan shekarun baya-bayan nan.

Ana amfani da irin wannan doka ne a wasanni kamar ƙwallon gora ta ƙanƙara inda a kan tanadi wani benci da ake aika 'yan wasan da suka yi wani laifi don su je su hutu na wani ɗan lokaci a yayin gasa.

Asalin hoton, MARTIN WATTERSTON

Bayanan hoto,

Wasanni irinsu ƙwallon gora ta ƙanƙara tuni suna amfani da irin wannan doka ta zauna-ka-huta

Idan aka amince da ita, za a fara amfani da dokar zauna-ka-huta a matakan gasar matasa da ƙwallon da ba ta ƙwararru ba, amma za a iya fara amfani da ita a gasar ƙwararru a cikin shekara biyu ko uku mai zuwa.

Sauran ƙudurorin da za a tattauna kansu a taron akwai bai wa hukumomin ƙwallon ƙafa damar tsaida shawara a kan yawan 'yan wasan da za su iya canji a gasa.

Matakin na da nufin taimaka wa bunƙasar harkokin ƙwallo a matakin ƙasa-ƙasa ta hanyar "ingantawa da ƙarfafa gwiwar ƙarin mutane su riƙa shiga ana damawa da su", a cewar sanarwar taron hukumar tsara dokokin.

Hukumar ta ƙunshi jami'an Fifa da hukumomin ƙwallon ƙafa na Burtaniya - wato Ingila da Scotland da Wales da Northern Ireland.