An ya akwai kulob din da zai iya kamo Chelsea?

Chelsea da Liverpool

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Diego Coasta ne ya samo kuma ya baras da fanaretin da Chelsea ta samu

Kunnen dokin da Chelsea ta yi 1-1 a gidan Liverpool ya sanya wasu na ganin kungiyar ta yi zarrar da ba za a iya cimmata ba a gasar Premier ta bana.

A yanzu Chelsea ta bai wa Tottenham da Arsenal da ke binta tazarar maki tara a teburin gasar.

Chelsea ce ta fara zira kwallo ta hannun David Luiz ta hanyar bugun tazara, inda ya shammaci golan Liverpool Simon Mignolet, kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Georginio Wijnaldum ne ya rama wa Liverpool minti 11 da dawowa daga hutun, abin da ya sa Liverpool ta kaucewa rashin nasara sau hudu a jere.

Dan wasan gaba na Chelsea Diego Costa, ya zubar da bugun fanareti ana saura minti 14 a tashi.

Arsenal, wacce ke mataki na uku, ta sha kashi a gida a hannun Watford da ci 1-2, yayin da Tottenham ta tashi babu ci tsakaninta da Sunderland.