Boko Haram ta kashe ma'aikatan MDD biyar a Kamaru

Jami'an tsaron Kamaru

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Arewacin Kamaru na fama da hare-haren Boko Haram

Majalisar Dinkin Duniya (MDD), ta ce wasu 'yan bindiga sun kashe ma'aikatanta biyar a wani hari da aka kai musu a kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Tawagar majalisar na aikin raba kan iyakar da ke tsakanin kasashen biyu ne.

MDD ta ce an kai harin ne ranar Talata a kusa da garin Kontcha da ke kan iyaka, inda kungiyar Boko Haram ta saba kai hare-hare.

Ta kara da cewa mutanan da lamarin ya ritsa da su sun hada da wani dan kwangila mai zaman kansa da 'yan Najeriya uku da kuma dan Kamarun daya.

Wakilin MDD na musamman a Yammacin Afirka, Mohamed Ibn Chambas ya yi tir da harin.

Babu wanda ya dauki alhakin harin kawo yanzu, amma kungiyar Boko haram na yawan kai hare-hare a yankin.