Trump na kare kasarsa daga hadari ne — Saudiyya

Saudi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Khalid Al-Faleh ya ce Amurka na kokarin kare 'yan kasarta daga hadari ne

Ministan man fetur na Saudiyya ya kare Shugaban Amurka Donald Trump kan tsaurara matakan shiga kasarsa da ya dauka, yana mai cewa "ko wacce kasa tana da damar kawar da duk wani abu mai hadari ga al'ummarta".

A wata hira da BBC a Riyadh babban birnin kasar, Khalid al-Falih, ya kuma ce yana da kwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba za a warware takaddama kan batun da ake ta ce-ce-ku-ce a kansa na hana wasu kasashe shiga Amurkan.

Mista Al'Falih ya ce yana kyautata zaton cewa Mista Trump ba zai aiwatar da alkawuran da ya dauka lokacin zabe ba na dakatar da sayen mai daga Saudiyya.

Ministan man ya ce kasashen biyu za su yi aiki kut-da-kut don tunkarar kalubalen da ke gabansu da kuma matsalolin da suka addabi duniya.

Haka kuma ministan ya yabi Mista Trump kan goyon bayan da ya nuna na amfani da makamashin kwal da iskar gas, yana mai cewa hakan zai karfafa tattalin arzikin kasashen biyu.

Ya kara da cewa tun a baya rashin alkiblar manufofin tsohon Shugaba Barack Obama, su suka hana a tsayar da magana kan wannan kuduri.

Me ya sa Trump bai hana 'yan Saudiyya shiga Amurka ba?

Tun bayan da Donald Trump ya sanya dokar hana wasu kasashen Musulmai bakwai shiga Amurka, duniya ta sha mamakin ganin cewa babu Saudiyya a jerin kasashen.

An samu rahotannin cewa daga baya zai sanya Saudiyyar ciki, saboda ganin cewa mutum 15 daga cikin 19 da suka kai harin 11 ga watan Satumba na 2001 Amurka 'yan Saudiyya ne.

Sai dai ga alama Shugaba Trump yana maraba da ci gaba da kawance da kuma huldar kasuwanci da Saudiyya kamar yadda tsohuwar gwamnatin Mista Obama ta yi.

Ministan man fetur na Saudiyyan ya ce, "Dole Amurka da Saudiyya muna bukatar tafiya tare da yin aiki da juna.

Ya kara da cewa "Ba za mu iya watsar da juna ba ko don karfafa tattalin arzikinmu".