Ana bin 'yar Nigeria da ta haihu a jirgin sama bashin miliyan 315

Dakin tiyata da likitoci
Bayanan hoto,

Dole Priscilla ta biya kudin kulawar da ake bata ita da yaranta asibitin.

Wani asibiti da ke Burtaniya na bin wata mata 'yar Najeriya da ta haihu a jirgin sama bashin $360,000 kwatankwacin naira 315 miliyan.

Priscilla ta shiga nakuda ne a jirgin wanda ke kan hanyarta ta zuwa Najeriya daga Amurka kuma ta haihu 'yan hudu a jirgin da ya sauka a fillin jiragen sama na Heathrow da ke Ingila.

Daga nan ne kuma aka garzaya da ita asibiti a birnin London, inda daya daga cikin jariran nata ya mutu baya ga dayan da ya mutu tun a cikin jirgin.

Kasancewar ba 'yar Birtaniya ba ce, dole ta biya kudin kulawar da ake bata ita da yaranta asibitin.

Yawan kudin da ake binta din ne kuma ya ja hankalin wasu daga ciki jaridun kasar, ko da yake jaridun The Sun da kuma The Daily Mail basu bayyana lokacin da ta haihun ba.

Bayanan hoto,

Priscilla ta hau wani Jirgin Amurka zuwa Najeriya a lokacin da ba ta da lafiya amma sai ta tsinci kanta a asibitin St Mary's

Gwamnatin Burtaniya bata biyan kudin kulawar gaggawar da aka ba wadanda ba 'yan asalin Ingila ba.

An yi kiyasa cewa an caji marasa lafiya wadanda ba 'yan kasar ba fam miliyan 289 a shekarar 2015 zuwa shekarar 2016, amma rabin kudin aka iya samu a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

Shirin BBC Two na talabijin wanda ke duba halin da asibitocin Burtaniya ke ciki zai tattauna a kan batun.