Rashin audugar mata ya hana zuwa makaranta

Audugan mata

Asalin hoton, KwaZulu-Natal Education Department

Bayanan hoto,

KwaZulu-Natal ta dauki matakin ne domin rage yawan 'yan matan da ke kin zuwa makaranta

Ana shirin raba wa 'yan mata da ke lardin KwaZulu-Natal a kasar Afirka ta Kudu audugar mata a duk lokacin da suka fara al'adarsu.

Lardin ya dauki wannan mataki ne domin rage yawan 'yan matan da ba sa zuwa makaranta saboda rashin audugar a lokacin da suke al'adar.

Wani bincike ya gano cewa miliyoyin 'yan mata 'yan kasar Afirka ta kudu, musamman wadanda basu da galihu, ba sa zuwa makaranta saboda ba za su iya sayen audugar ta mata.

Hukumar kula da ilimi ta KwaZulu-Natal ta ce za ta bai wa 'yan mata audugar a makarantu kusan 3,000 da ke lardin.

A karkashin wannan shirin dai za a bukaci shugabar makaranta ko wani jami'i ya sanya hannu a takarda bayan karbar audugar.

Hukamar ta ce, "Ba mu yarda kanwar mahaifiya ko kuma wata 'yar uwa ta yi amfani da audugar ba."

Ta kara da cewa an dauki matakin ne saboda a tamaika wajen inganta ilimin mata kuma a tabbatar da cewa ba sa kin zuwa makaranta saboda ba za su iya sayen audugar mata ba.

An yi kiyasin cewa mata masu shekaru tsakanin 13 da 19 a Afirka ta Kudu su kan yi mako guda ba su je makaranta ba a kowanne wata, a lokacin da suke al'ada saboda ba su da kudin da za su sayi auduga.