An taso keyar 'yan Nigeria 40 daga Birtaniya

Kayan mutnanen da aka taso kyayarsu

Asalin hoton, Smile Baba

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin mutanen za su ci gaba da zama a gidan kaso har sai sun kammala wa'adinsu

A safiyar ranar Laraba ne dai wasu 'yan Nigeria kimanin 40 wadanda aka tasa keyarsu daga Birtaniya suka iso filin jirgin saman Lagos.

A cikin mutane 40 din wadanda hukumar shige da fice ta kasa ta tabbatar an dawo da su kasar, har da mata da tsofaffi da kuma fursunoni.

Hukumar da ma wasu Jami'an tsaron Najeriya wadanda suka hada da 'yan sanda, sun halarci filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Lagao domin tarbar mutanen.

Wakilinmu da ke Lagos ya shaida mana cewa babu wani karin bayani da hukumomi suka yi game da laifukan da suka aikata.

Sai dai a cikinsu akwai wadanda suka fara zaman gidan kaso tun suna Birtaniyan kuma zasu ci gaba da zama a jarun har sai sun kammala wa'adin da aka dibar musu.

Mutanen da dama sun iso cikin wani irin mawuyacin hali inda wasu daga cikinsu suka nuna alamun galabaita.