Afghanistan: Wani ya yanke wa matarsa kunne

Zarina
Bayanan hoto,

Zarina tana samun sauki a asibiti

Wata matashiya 'yar kasar Afghanistan mai shekara 23 ta bayyana wa BBC yadda mijinta ya daure ta kuma ya yanke mata kunnuwa a arewacin lardin Balkh.

Zarina tana samun sauki sai dai tana cikin halin kaduwa a asibiti.

Ta ce, "Ban aikata wani laifi ba. Ban san dalilin da ya sa mijina ya yi min haka ba."

'Yan sanda sun shaida wa manema labaran kasar cewa mijin Zarina ya gudu daga gundumar Kashinda bayan da ya aikata laifin.

Zarina ta shaida wa kafar yada labarai ta Pajhwok cewa mijnta ya yi mata wannan aika-aika ne bayan ya tashe ta daga barci.

Ta shaidawa BBC cewa ta yi aure tana da shekara 13 kuma babu kyakkyawar dangantaka tsakaninta da 'yan unwan mijinta.

A wata hira da ta yi da kafar yada labarai ta Tolo, Zarina ta yi korafin cewa maigidanta ya yi kokarin hana ta zuwa wurin iyayenta.

Ta ce ba ta so ta ci gaba da auren shi.

Bayanan hoto,

Zarina ta ce bata so ta cigaba da aure tsakaninta da mijinta

"Mutum ne mai yawan zargi kuma yana yawan zargi na da yi wa wasu mazan magana duk lokacin da na ziyarci iyayena", a cewarta.

Ta bukaci a kama shi kuma a tuhume shi da laifi.

Labarin Zarina shi ne labari na baya-bayan nan a dumbin labaran cin zali a kan mata a kasar Afghanistan.

Gwamnatin kasar dai ta yi yunkuri a lokuta da dama ta gabatar da dokoki domin kare mata daga zalunci a gidajen aurensu.

Amma a lokacin da Shugaba Hamid Karzai ya ke kan mulki, bai yi wata hobbasa ba wajen ganin cewar an zartar da dokar duk da cewa 'yan majalisar dokokin kasar sun amince da kudirin dokar.

Bayanan hoto,

Labarin Zarina na cikin dumbin labaran cin zali da mata ke fuskanta a gidajen aurensu a Afghanisatan

Ashraf Ghani, wanda ya maye gurbin Mista Karzai, shi ma har yanzu bai amince da kudurin dokar da majalisar wakilai ta zartar a watan Nuwamba da kuma wanda majalisar dattawa ta zartar a watan Disamba ba.

Majalisun sun zartar da kudurin dokar ne domin bai wa mata kariya daga cin zali da zarafi da suke fuskanta a kasar.