Gwamnatin Nigeria 'na kokarin rage farashin abinci'

Shugaba Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari na shan suka kan yadda yake tafiyar da tattalin arzikin kasar

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani kwamiti da zai duba yadda za a inganta hanyoyin samar da abinci a kasar da kuma saukar da farashinsa a kasuwanni.

Makaddashin shugaban kasar Yemi Osinbajo ya ce an dauki matakin ne domin magance matsalar tsadar kayan abinci da kasar ke fama da ita a baya-bayan nan.

Farashin kayayyaki sun yi tashin gwauron zabi, abin da ya kara jefa 'yan kasar cikin mummunan hali.

Najeriya na fuskantar matsalar tattalin arziki mafi muni cikin shekara 20 sakamakon faduwar darajar danyan mai a kasuwannin duniya.

A lokacin da ya ke bayar da umarni a wata ganawa da ya yi da majalisar zartarwa, Mista Osinbajo ya nuna damuwarsa a kan hauhawar wasu kayayyakin abinci.

Ya ce kwamitin da aka kaddamar zai ta duba hanyoyin da za a bi domin inganta samar da abinci a farashi mai sauki ga 'yan Najeriya.

Duk da rahotannin da ke cewa amfanin gonaki sun yi yabanya a sassa daban-daban na kasar, farashin abinci na kara hawa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Farashin kayayyaki sun fara tashin gwauron zabi tun watan Fabrairun 2016

Wasu kayan amfanin gonar kuma na lalacewa sakamakon rashin ingantacciyar hanyar da za a bi domin sufurin kayan zuwa kasuwanni ko kuma adana su.

A cewarsa, kwamitin wadda aka bai wa wa'adin kwana bakwai daga ranar Laraba domin gabatar da rahotonta, zai duba yiwuwar kawar da abubuwan da ke haddasa hauhawar farashi a tsakanin gonaki da kasuwanni.

Mista Osinbajo ya ce yin haka zai kawo sauki ga al'ummar kasar.

Farashin wasu abubuwa a watan Janairun 2016 zuwa Janairun 2017

  • Buhun shinkafa babba N8000 - N19,500
  • Buhun Semovita N1,300 - N3000
  • Buhun fulawa N6,000 - N12,000
  • Kwanon dawa - N140 - N600
  • Kwanon wake N400 - N800
  • Kwanon sikari N400 - N900
  • Indomie N35 - N70
  • Tulun gas matsakaici (kilo 12.5) N2,500 - N5,300
  • Litar kananzir N100 - N500

Kwamitin na karkashin ministoci kamar haka:

Ministan Gona Chief Audu Ogbeh

Minisar Kudi Misis Kemi Adeosun

Ministan Kasuwanci Okey Enelamah

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi

Ministan Ruwa Suleiman Adamu

Ministan Kwadago Chris Ngige