DRC: Madugun 'yan adawa Tshisekedi ya rasu

Etienne Tshisekedi
Bayanan hoto,

Tshisekedi ya rasu ya na da shekaru 84, ya yi gwagwarmayar siyasa da shugaba Laurent Kabila

Fitaccen dan siyasa kuma madugun 'yan adawa a Jamhuriyya Dimukradiyyar Congo Etiyan Shisekedi ya rasu a kasar Belgium ya na da shekaru tamanin da hudu a duniya.

Mukaddashin sakataren jam'iyyar UDPS ta mista Etienne Rubens Mikindo ne ya sanar da mutuwarsa.

Dubban magoya bayansa ne sukai dafifi a kofar gidan dansa Felix dan nuna alhinin mutuwarsa.

Mista Shisekedi ya rike manyan mukamai tun bayan karbar yancin kai da kasar ta yi daga hannun Belgium a shekarar 1960, ciki har da Firai ministan kasar.

Ya taba zaman jarun na dan wani lokaci, daga bisani kuma ya bar kasar a lokacin mulkin shugaba Laurent Kabila ya kuma zama babban mai sukar gwamnatin dan shi wato Joseph Kabila.