Lagos: Hukuncin kisa kan masu satar mutane

Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An iyana hukuncin kisa a Najeriya

Gwamnatin Lagos da ke Kudancin Najeriya, ta ayyana hukuncin kisa a kan masu satar mutane domin kudin fansa.

Gwamnatin ta ce yawan satar mutane da ake yi don neman kudin fansa ya kai wani matsayi da ake bukatar a dauki matakin gaggawa.

Sabuwar dokar, wadda gwamnan jihar Akinwunmi Ambode, ya rattabawa hannu ta ce, idan mutane suka mutu a hannun wadanda suka sace su to su ma za a kashe su.

Wannan shi ne karon farko da jihar Lagos ke ayyana hukuncin kisa a kan masu satar mutane.

Dokar ta kuma gabatar da hukuncin daurin rai da rai ga masu satar mutane domin karbar kudin fansa.

A halin yanzu, satar mutane ya zama wani babban kalubale da 'yan Najeriya ke fuskanta.

A watan Oktobar bara ne dai aka sace wasu dalibai hudu da mataimakin shugaban makaranta da wasu malaman makarantar Lagos Model da ke Epe.

Wannan doka na zuwa ne watanni shida bayan an sace dalibai mata uku daga makarantar Babington Macaulay Junior, da ke Ikorodu a jihar ta Lagos.

Baya ga haka, a makonni biyu da suka wuce, an sace dalibai uku na makarantan Turkish International, da wasu ma'aikatansu a jihar Ogun, makwabciyar Lagos din.

Gwamnan Jihar Lagos ya ayyana dokar ne da nufin yin gargadi sannan hakan ya zama izina ga wadanda ke da niyyar aikata irin wannan laifi.