India: Me ya sa ake kin taimaka wa wadanda suka yi hatsari?

Likitoci a asibiti
Bayanan hoto,

Idan hatsari ya auku mutane kan tamaika wa wadanda lamarin ya shafa amma wasu kan ki yin hakan a Indiya

Bidiyon wani matashi a India da ya mutu saboda mutanen da suka taru, ba su taimaka masa ba lokacin da ya yi hatsari ya yi matukar tayar da hankalin'yan kasar.

Kafofin yada labarai sun ruwaito cewar mutane sun taru suna kallo da kuma daukar hotuna da bidiyon matashin wanda ya jikkata, amma kuma ba su kai shi asibiti ba.

An kai Anwar Ali mai shekara 17 asibiti sa'a guda bayan da kekensa ya ci karo da wata babbar mota a jihar Karnataka da ke Indiya.

Anwar ya yi ta zubar da jini har sai da ya mutu. Likitoci sun ce tana iya yiwuwa ya rayuwa idan ya samu kulawar gaggawa bayan da lamarin ya faru.

Lamarin da ya faru a gundumar Koppal da ke Karnataka ya jawo ce-ce-ku-ce a kan yadda mutane ke nuna halin ko-in-kula ga wadanda suka yi hatsari a Indiya.

Wasu masu rajin kare hakkin dan'adam sun ce ba rashin tausayi ba ne amma al'umma ce ta juyawa wanda yake bukatar taimako baya.

"Dalilin farko shi ne tsoron kada 'yan sanda su tutsiye mutum," kamar yadda Piyush Tewari ya shaida wa BBC.

Baya ga tsoron cewar 'yan sanda za su iya dora wa mutum laifin da ba nasa ba, mutane na tsoron kada a nemi su bayar da shaida idan aka shigar da kara kotu.

Kuma idan suka kai wanda ya yi hatsari asibiti, suna tsoron za a matsa musu lamba sai sun biya kudin jinya.

A watan Mayun bara ne kotun kolin Indiya ta yanke shawarar cewa za a kare duk wani bawan Allah da ya bayar da agaji daga fuskantar matsin lamba.