An cimma yarjejeniyar kawar da satar dabbobi a Zamfara

Janar Buharin Daji Shugaban kungiyar masu satar dabbobin
Bayanan hoto,

Mutane da dama sun rasa rayukansu sakamon rikici tsakanin masu satar dabbobi da makiyaya

A jihar Zamfara ta Najeriya an yi shelar cimma yarjejeniya dakatar da hare-hare da kuma samun zaman lafiya tsakanin 'yan bindigar da ke kai hare-hare kan kauyuka, da kuma 'yan banga daga kauyukan da su ma ke kai musu hari a wasu lokutan.

Dubban mutane ake jin sun mutu a rikicin da aka kwashe fiye da shekaru biyar ana yi a sassa daban-daban na jihar.

An dai sanar da cimma yarjejeniyar ne ranar Alhamis a wajen wani taro tsakanin bangarorin biyu da shugabannin siyasa, da tsaro da kuma sarakunan jihar da ke shiga tsakani.

Sharuddan yarjeniyar sun hada da mika makamai da daina yawo da su a ko'ina, da mayar da dukiyoyi da gonakin da ko wanne bangare ya kwace daga dayan, da kuma bari mutanen da ko wanne bangare ya kora daga matsugunansu su dawo.

A cikin wata hira da BBC mai jagorantar tattaunawar kuma mataimakin gwamnan jihar Ibrahim Wakkala, ya ce gwamnatin jihar ta kafa kwamiti domin tallafa wa wadanda suka rasa danginsu da kuma kadarorinsu.

Ya ce nan gaba kadan za a gudanar bukin kawo karshen fadace-fadacen wanda ake sa ran shugaban kasar zai halarta.

Shugaban kungiyar masu satar dabbobi, Janar Buharin Daji, ya hallarci taron.