An ci Facebook tarar dala miliyan 500 a Amurka

Mark Zuckerberg

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ribar da Facebook ya samu a karshen bara ta kusa dala biliyan hudu

Wata kotu a Amurka ta umarci kamfanin Facebook da wasu masu kare kansu su biya tarar dala miliyan 500 bayan ta gano cewa sun saci manhajar wasu kamfanonin wajen kirkirar hotuna da bidiyo na hakika.

Masu taimaka wa alkali yanke hukunci sun samu kamfanin Oculus, wanda Facebook ya saya a shekarar 2014, da laifin saba yarjejeniyar kwantiragin da ya kulla da kamfanin Zenimax.

An kulla yarjejeniyar ce a lokacin da yake kaddamar da na'urarsa ta saurare da kallon wasannin video wadda ake sakalawa a ka.

Kamfanin Oculus ya ce bai "ji dadin hukuncin ba" kuma zai daukaka kara.

Wannan shari'a ta so ta dauke hankali daga ribar Facebook ta baya bayan nan, wadda ke nuna cewa kasuwa ta yi masa kyau zuwa karshen bara.

Ribar da Facebook ya samu bayan biyan haraji a watanni hudun karshe na shekarar dai ya ninka abin da ya samu kafin nan, ya kai dala biliyan uku da miliyan dari shida.

Wannan ribar ta shafin na sada zumunta dai ta samu ne da taimakon karuwar da kudin shigarsa daga tallace-tallace ya yi da kashi hamsin da uku cikin dari, kuma ya ce yawan masu amfani da shafin na daf da kaiwa biliyan biyu a watanni shida na farkon 2017.

'Sirrin Facebook'

Jim kadan kafin bayanan ribar kamfanin sun bayyana, kotun ta bukaci kamfanin Facebook da Oculus da kuma manyan jami'an Oculus su biya diyya ga kamfanin Zenimax bayan an shafe makwannin uku ana sauraron shari'a.

Zenimax ya kafa hujja da cewa kamfanonin sun saci fasahar da ya kirkira ta wasannin bidiyo don yin tasu na'urar da ake sakalwa a ka mai suna Rift.

"Mun yi farin ciki da masu taimaka wa alkali yanke hukunci a Kotun Gunduma dake Dallas suka ba da umarni a biya Zenimax diyyar dala miliyan dari biyar saboda satar fasaharmu da wadanda ake tuhuma suka yi", in ji shugaban kamfanin Zenimax Robert Altman.