'Ba za mu hakura da diyyarmu ba'

Hissene Habre

Asalin hoton, CAE

Bayanan hoto,

Hissene Habre ya ki magana da lauyoyin da kotu ta ba shi don su kare shi a shari'a

A kasar Chadi wasu wadanda suka fuskanci cin zarafi a lokacin mulkin tsohon shugaba Hissene Habre a shekarun 1980, sun ce ba za su hakura da fafutukar neman diyyar da aka yi musu alkawari ba.

An yanke wa Hissene Habre hukunci a kan laifuffukan yaki, da cin zarafin bil'adama, da azabtarwa a wata kotu ta musamman da ke kasar Senegal a watan Mayun bara.

An kuma umarce shi ya biya kowanne mutum guda diyyar dala $34,000, amma kuma har yanzu kotun ba ta iya gano inda kudaden tsohon shugaban suke ba.

Wani daga cikin mutanen da aka gana wa akuba a zamanin gwamnatin Habren, Younous Mahadji wanda a lokacin dalibi ne, amma kuma yanzu likita ne a babban asibiti N'Djamena ya bayyana irin azabar da jami'an tsaro suka yi masa a lokacin.

Ya ce a shekarar 1990 lokacin yana dalibi, an zarge shi da laifin raba takardun sakonnin kin jinin gwamnati.

Saboda haka ne jami'an tsaro suka rika azabtar da shi, ta hanyar daure hannuwansu da kafafunsa ta baya, har tsawon wata hudu.

Ya kara da cewa a lokacin da aka tsare shi a gidan yari nauyinsa ya kai kilo 75, amma bayan wata hudu sai ya zabge zuwa kilo 40, bayan Habre ya tsere daga Chadi.

Bayanan hoto,

An zargi Hissene Habre da cin zarafi da take hakkin bil'adama a lokacin mulkinsa

A watan Janairu na 2017 lauyoyin da kotu ta nada wa Habre domin kare shi, wadanda ya ki ya yi magana da su, suka daukaka kara kan hukuncin da aka yanke masa.

Kuma a watan Afrilu ne ake sa ran yanke hukunci kan daukaka karar, kuma ana ganin abu ne mai wuya daukaka karar ta yi nasara.