'Za mu iya daukar matakin soji a kan Iran'

Shugaba Donald Trump

Asalin hoton, Xinhua

Bayanan hoto,

Donald Trump daman yana ta sukar yarjejeniyar nukiliyar da aka yi da Iran

Shugaba Donald Trump ya ce komai zai iya wakana a martanin da ya yi game da cewa ko zai iya daukar matakin soji kan Iran a kan gwajin makami mai linzami da ta yi.

Fadar gwamnatin Amurka, White House ta ce, kasar za ta mayar da martani a kan gwajin makami mai linzamin amma ba ta bayar da karin bayani ba.

Tun da farko wani babban jami'in gwamnatin ya yi watsi da barazanar ta gwamnatin Trump da cewa shirme ne kawai.

Ali Akbar Velayati, wanda babban mai bayar da shawara ne ga shugaban addini na Iran din, Ali Khamenei ya ce wannan ba shi ne farko ba da wani dandagaji yake barazana ga Iran ba.

Wannan ce irin ce-ce-ku-cen da ta rika kasancewa a alaka tsakanin Amurka da Iran, har dai a karshe aka kai ga samun kammala yarjejeniyar kasashen duniya da aka yi ta sa-toka-sa-katsi a kan batun shirin nukiliyar Iran, sama da shekara daya.

To amma ga alama ba lalle hakan ta kasance ba yanzu a karkashin shugabancin Donald Trump, wanda ya sha sukan wannan yarjejeniya.

Ita dai Iran ta kafe cewa gwajin makami mai linzamin da ta yi a karshen mako, bai karya sharuddan wannan yarjejeniya ba.

Amma kuma duk da haka ana ganin wata tsokana ce, a daidai wannan lokaci na 'yan kwanaki da zuwan gwamnatin Trump.

Ana ganin gwajin kamar wata barazana ce da Iran ke yi ga makwabtanta, wadanda suka hada da kawayen Amurka a yankin.

Kuma kamar yadda aka yi tsammani, lamarin ya jawo kakkausan martani daga gwamnatin Donald Trump din.

Sai dai ya zuwa yanzu, maganar fatar baka ce kawai, amma kuma gaba kadan abin da ya zarta haka ka iya biyo baya.